Monday 22 December 2025 - 12:04
Sheikh Zakzaky (H) ya dawo Najeriya bayan ziyarar qarin Ilimi da Ma'anawiyya zuwa Iran

Hauza/ Jagoran Harakatul Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky (H), ya dawo gida Najeriya bayan kammala gajeren bulaguron da ya yi zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.  

Rahoton sashen fassarar labarai na Hauza ya tabbatar da cewa, Sheikh Zakzaky (H) ya dawo gida a ranar Jumma’a, 19 ga Jumada al‑Thani, shekarar 1447 Hijiriya, wanda ya yi daidai da19 ga Disamba, 2025 Miladiyya, bayan kammala Bulaguron sa na musamman.

An bayyana cewa manufar wannan tafiyar ita ce halartar wani taron girmamawa, inda Sheikh Zakzaky tare da wasu fitattun malaman addini, suka samu lambar yabo saboda rawar da suke takawa wajen yada tunanin Imam Ruhullah al‑Khomeini (Ra) a fadin duniya.

Wannan tafiya, bisa ga rahoton, ta kasance cike da albarka, darussa masu muhimmanci, da kuma karin haske kan hakikanin manufa, wanda hakan ya sanya tana da matuƙar muhimmanci ga mahalarta taron.

Haka kuma, a yayin wannan ziyarar, Sheikh Zakzaky ya gana da Ayatollah Qomi, inda a wajen taron, aka gabatar da Hujjatul Islam wal Muslimin Mahdavi‑Fur ya amatsayin wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (Ayatollah Khamenei) a nahiyar Afirka.

Majiya: kafar sadarwa ta cibiyar Al‑Basir — Harakar Musulunci, Qom, Iran.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha